Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAkpabio ya bukaci musulmai da su yi wa kasa addu’ar zaman lafiya...

Akpabio ya bukaci musulmai da su yi wa kasa addu’ar zaman lafiya a lokacin azumi

Yayin da aka fara gudanar da watan azumin Ramadan, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira ga Musulmai da su yi amfani da wannan lokaci wajen addu’a don zaman lafiya a Najeriya da duniya baki daya.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ga ‘yan jarida a jiya a Abuja ta bakin mashawarcin sa na musamman kan harkokin yada labarai, Hon. Eseme Eyiboh, Akpabio ya bukaci mabiya addinin Musulunci da su yi amfani da muhimmancin watan Ramadan ta hanyar nuna tausayi, karfafa fahimtar juna, da inganta hadin kai.

“Yayin da al’ummar Musulmi ke shirin gudanar da ibada a watan azumin Ramadan, ina mika gaisuwada fatan alheri ga dukkan Musulmai a Najeriya da duniya baki daya,” a cewar sakon.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments