Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiKundin tsarin mulki ya bani damar shiga harkar siyasa – Sheikh Pantami

Kundin tsarin mulki ya bani damar shiga harkar siyasa – Sheikh Pantami

Pantami ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar Gwamnan Gombe

A ƴan kwanakin baya-bayan nan an yi ta muhawara musamman a kafofin sada zumunta kan batun siyasar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Farfesa Ali Isa Pantami.

A farkon watan Fabarairu ne tsohon ministan sadarwar na Najeriya ya sake motsa siyasarsa bayan ya je harabar sakatariyar jam’iyyar APC a jihar Gombe inda ya sabunta rajistarsa.

Sheikh Pantami ya kuma zagaya sassan birnin Gombe bisa rakiyar dubban magoya bayansa a wani mataki na nuna neman goyon bayan jama’a.

Duk da kasancewar Farfesa Pantami tsohon minista a gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, da dama ƴan ƙasar ba sa yi masa kallon ɗan siyasa, a maimakon haka suna ganin Buhari ya naɗa shi muƙamin ne sanadiyyar ƙwarewarsa a fannin fasahar sadarwa.

Ana dai alaƙanta fitaccen malamin addinin da tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Pantami ya bayyana dalilansa na shiga siyasa gadan-gadan.

Sheikh Pantami ya ce ya jima da shiga siyasa, kuma a matsayinsa na dan Najeriya kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi damar shiga harkokin siyasar ƙasar.

”Da farko ma kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa ba za ka taba zama minista a ƙasar nan ba sai kana da katin jam’iyya”, in ji malamin.

Don haka malamin ya ce a yanzu duk wanda yake riƙe da muƙamin minista, in dai ba shi da katin jam’iyya to ya saɓa wa doka.

⁩

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments