Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaRashin fitar da sunayen ƴan takara da wuri zai iya haifar da...

Rashin fitar da sunayen ƴan takara da wuri zai iya haifar da rikici a Kano – INEC

INEC ta bayyana cewa jinkiri fitar da yan takara ka iya hai far da rikici a Kano

Hukumar zaɓe ta INEC a jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da hurumin yin karin bayani kan takaddamar da ta kaure tsakanin jam’iyyun APC da NNPP kan gabatar da sunayen ‘yan takara guda daya a zaɓen cike gurbi na ‘yan majalisar dokokin jihar.

Shugaban hukumar zaɓe reshen jihar, Ambasada Abdu Zango, ya ce, “hedikwatar INEC ce kaɗai ke da damar wallafa sunayen ‘yan takara da jam’iyyarsu,” inda ya bayyana cewa ba zai iya bayyana sunayen da jam’iyyun suka gabatar ba a wannan mataki.

Ambasada Abdu Zango ya ƙara da cewa babban aikin reshen hukumar shi ne tattara bayanan ‘yan takara, haɗa rahoto, sannan a miƙawa hedikwatar hukumar don wallafa su.

Ya kara da cewa nan gaba kaɗan, INEC za ta fitar da sunayen ta intanet domin jam’iyyun siyasa da al’umma su samu cikakken bayani.

Masu sharhi kan harkar siyasa sun nuna damuwa cewa wannan jinkirin wallafa sunayen na iya haifar da karin rikici tsakanin jam’iyyun, musamman yayin da lokacin shirye-shiryen kamfen ke ƙaratowa.

Wasu ‘yan siyasa na ganin cewa INEC na bukatar ta hanzarta wallafa sunayen domin tabbatar da gaskiya da adalci a zaɓen cike gurbi.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments