Shugaban Amurka, Donald Trump ya sake yi wa Iran barazanar ɗaukar matakin soja, inda yake matsa wa ƙasar lamba don ta tattauna kan yarjejeniyar makaman nukiliya.
Mista Trump ya ce wani babban jirgin rundunar sojin Amurka na tunkarar ƙasar, yana mai barazanar cewa harin da zai kai mata nan gaba zai ninka irin wanda ya kai mata a 2025 Yuni.
Iran ta dage cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, tana mai gargaɗin cewa duk wani hari da Amurka ta kai mata na iya jefa rayukan dukkannin dakarunta da ke Gabas ta Tsakiya a cikin haɗari.
A Majalisar Dinkin Duniya, China ta yi gargadi game da barazanar ta Amurka.
Wannan na faurwa ne bayan zargin kisan dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnati da aka yi a Iran.