Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiTrump ya yi gargadin kawo wa Iran zazzafan harin da yafi wanda...

Trump ya yi gargadin kawo wa Iran zazzafan harin da yafi wanda ta kai mata a baya

Shugaba kasar Amurka Donald Trump ya ce lokaci na ƙurewa gwamnati Iran na hawa teburin tattaunawa.

A cewar sa idan gwamnatin ta gaza hakan, ya yi gargaɗin cewa hari na gaba da zai kai mata, zai fi wanda da aka kai cibiyoyin nukiliyarta a watan Yunin 2025.

Mista Trump ya ce wasu manyan jiragen ruwan yaƙi na tunkarar Iran, inda ya ce a shirye suke su kammala aikinsu cikin gaggawa, kamar yadda dakarun Amurka suka kai hari Venezuela.

Tun da farko dai ministan harkokin wajen Iran ya ce bai yi wata tattaunawa da Amurka ba a kwanakin baya bayan nan, kuma bai buƙaci a yi wata tattaunawa ba.

Sai dai Abbas Araqchi ya ce masu shiga tsakani da dama, waɗanda bai bayyana sunayensu ba, na neman shawarwari da kuma ganawa a Tehran.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments