Kamfanin NNPCL da ke kula da albarkatun mai na Najeriya ya sanar da gano wata sabuwar rijiyar mai a gabashin gaɓar tekun yammacin yankin Neja Delta mai arziƙin mai.
Tuni dai NNPCL ya yiwa rijiyar suna da Awodi-07, wadda gano ta ke zuwa a dai dai lokacin da Najeriyar ke ƙoƙarin ganin ta ƙara yawan man da ta ke iya haƙowa a kowacce rana,duk da gamuwa da tarin matsaloli.
Babban jami’in yaɗa labaran kamfanin NNPCL Andy Odeh da ke sanar da wannan nasara ta gano sabuwar rijiyar mai cikin wata sanarwa da ya sanya a shafin kamfanin tun a Litinin ɗin da ta gabata, ya ce babban tagomashi ne ga ƙasar.
Duk da kasancewar Najeriya a sahun ƙasashe masu arziƙin man fetur, amma matsaloli alaƙa da ayyukan tsageru a yankin na Neja Delta da ke fasa bututu da kuma masu zagon ƙasa ga ayyukan haƙar man sun yi ƙasar katutu, hakan ya hana ta iya fitar da adadin da ake buƙatar ta samar kowacce rana a kasuwar duniya ƙarƙashin tanadin OPEC.