Tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa a shirye yake ya shirya da babban abokin siyasarsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya ce, “Ina fatan nan gaba za mu daidaita da Kwankwaso, a tafi baki ɗaya domin harka ce ta siyasa.
“Da mun yi siyasa tare da shi, mu ‘yan uwan juna ne.”
Ganduje da Kwankwaso dai sun jima ba sa ga maciji da juna a harkokin siyasar jihar Kano, kuma ana ganin komawar da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi zuwa jam’iyyar APC zai sake ruruta ƙiyayyar da ke tsakaninsu.
Ganduje ya ce abin da yanzu ya fi muhimmanci shi ne ci gaban al’ummar Kano da kuma nasarar jam’iyyar APC.
“Da an yi hamayya, yanzu ana tare. An riga an rufe wancan shafi.”
Abin da aka sa a gaba shi ne ci gaban al’ummar Kano da samun nasara a wannan jam’iyya,” in ji shi.
Ya kara da cewa, “Idan Abba ya samu nasara, mun samu; in mun samu nasara, ya samu; idan ya faɗi, mun fadi; idan mun fadi, ya fadi.
Duk wanda ya gane wannan, magana ce ta mu taimaka wannan gwamnati tayi nasara.”
Ganduje ya bayyana cewa kasancewarsa tsohon shugaban jam’iyyar APC na tsawon shekara biyu ya ba shi damar fahimtar tsarin jam’iyya da yadda ake tafiyar da al’amuranta.
“A kan batun ko za a ba Abba dama ya tsaya takara a jam’iyyar, na san abun da yaka a tsarin mulki da kuma abin da yake na al’ada na jam’iyyar.
Ganduje ya jaddada cewa hadin kai tsakanin shugabannin jam’iyya da ‘yan siyasa zai taimaka wajen samun nasara a jihar Kano.