Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana da yaƙinin cewa sai gwamnan Kano Abba Kabir da muƙarrabansa sun yi da-na-sanin fita daga jam’iyyar NNPP da suka yi.
Sanata Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga jam’iyyar NNPP ta zo da ba-zata ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.
”Da yawa mutane ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su.
Nima sau da yawa ba na yarda cewar abubuwan da suke faruwa haka su ke.” in ji Kwankwaso.
A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma’a 23 ga watan Janairun 2023, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikinta.
A wajen bikin komawarsa APC, gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin sauya sheƙar ne bisa la’akari da inda aka dosa a siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da za ta kawo ci gaba ga jama’ar Kano baki ɗaya.
Ya kuma ce sai da ya tuntuɓi tsakanin abokan tafiyarsa a siyasance da sauran masu ruwa da tsaki kafin yanke hukuncin sauya sheƙar.