Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNajeriya da Turkiya sun ƙulla kasuwancin $5bn

Najeriya da Turkiya sun ƙulla kasuwancin $5bn

Kasar Turkiya da kulla yarjejeniyar kasuwanci da Najeriya

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa ƙasarsa na da burin ƙara yawan cinikayya da Najeriya zuwa $5bn, daga $2bn.

Shugaba Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a birnin Ankara, yayin taron manema labarai na haɗin gwiwa da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a ziyarar aiki da Tinubu ya kai ƙasar.

Erdogan ya ce tuni aka fara tattaunawa domin cimma wannan buri, inda ya bayyana cewa Turkiyya na fitar da jiragen sama da jirage masu saukar ungulu da injuna da ƙarafa da sinadarai zuwa Najeriya, yayin da Najeriya kuma ke fitar da ɗanyen mai da kayayyakin gona zuwa Turkiyya.

Ya kara da cewa ƙasashen biyu sun tattauna batutuwa da suka shafi cinikayya da zuba jari da makamashi da ilimi da masana’antar tsaro, tare da nuna fatan haɗin gwiwa tsakanin kamfanin man fetur na Turkiyya da na Najeriya zai haifar da sakamako mai kyau.”

Erdogan ya kuma yi alkawarin tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci, musamman ganin yadda matsalar ta’addanci ke barazana ga yankin Sahel da nahiyar Afirka baki ɗaya.

A nasa jawabin, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gode wa Turkiyya bisa shirinta na haɗin gwiwa da Najeriya domin bunƙasa ‘yanci da zaman lafiya da wadata a duniya.

Ƙasashen biyu dai sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi tara, ciki har da na tsaro da na cinikayya da ilimi da kafofin watsa labarai da harkokin mata da jinƙai, domin ƙarfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Turkiyya.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments