Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAmurka: Jami'an ICE sun harbe wani mai zanga-zanga har lahira

Amurka: Jami’an ICE sun harbe wani mai zanga-zanga har lahira

Jami’an kasar Amurka sun harbe wani mai zanga-zanga

Jami’an tsaro na gwamnatin tarayya a Amurka sun bindige wani mutum mai zanga-zanga a birnin Minneapolis ranar Asabar.

Wannan dai shi ne mutum na biyu da aka kashe a birnin tun lokacin da gwamnatin Trump ta ƙaddamar da wani yaƙi na musammman kan ƴan cirani a jihar ta Minnesota.

Jami’an yankin sun bayyana sunan mutumin a matsayin Alex Pretti mai shekaru 37, ɗan ƙasar Amurka ne kuma ma’aikacin jinya da ke zaune a Minneapolis.

A cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda jami’an tsaron suka kai mutumin ƙasa.

Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) ta ce jami’an sun yi harbi ne domin kariyar kai bayan Pretti, wanda suka ce yana da riƙe da bindiga, ya bijirewa yunƙurinsu na ƙwace masa makamai.

Lamarin, wanda ya zo makonni biyu bayan harbe Renee Nicole Good da wani jami’in shige-da-fice ya yi, ya haifar da ci gaban zanga-zanga tare da kiraye kiraye da shugabannin yankin cewa jami’an tsaron gwamnatin tarayya su fice daga birnin.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments