Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaFicewar Gwamna Abba daga Kwankwasiyya cin amanar al’umar Kano ne – NNPP

Ficewar Gwamna Abba daga Kwankwasiyya cin amanar al’umar Kano ne – NNPP

NNPP ta mayarwa da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf martani kan ficewa daga jam’iyyar

Jam’iyyar NNPP ta yi kakkausar suka kan matakin da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri’ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na 2023.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar, jam’iyyar ta ce matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka tamkar cin amanar al’ummar jihar Kano ne, wanɗanda a cewarta, sun kaɗa masa ƙuri’a ne sakamakon daɗewar da ya yi yana tare da tafiyar siyasar Kwankwasiyya.

”Muna matuƙar takaicin yadda Gwamna Abba, mutumin da al’ummar Jihar Kano suka damka wa al’ummar Jihar kan karfin biyayya da sadaukarwar da ya yi na tsawon shekaru da dama da ya yi wa tafiyar Kwankwasiyya, a yanzu ya zaɓii ya ci amanar da aka miƙa masa.” in ji sanarwar.

Ta kuma ƙara da cewa:

”Wannan mataki na iya mayar da jihar hannun waɗanda suka daɗe suna adawa da ci gabanta da muradun al’ummarta.”

Jam’iyyar NNPP ta buƙaci magoya bayanta a Kano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka, su kuma yi taka-tsan-tsan kan duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma a siyasance ko kuma ta da zaune tsaye.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments