Tarin mazauna yankin Yelwa a Jihar Bauchi sun hallara a wajen bikin shan rake na shekara-shekara karo na 11.
A cewar Albarka Radio Bauchi, bikin ya jawo hankalin jama’a daga Unguwar Yelwa da maƙwabtan al’ummomi, inda aka gabatar da jawabai daban-daban.
Babban Limamin Masallacin Juma’a ya gabatar da huduba kan muhimmancin zumunci da haɗin kai a Musulunci, yayin da wani likita ya yi bayani kan amfanin shen rake ga lafiyar ɗan Adam.