Adadin mutanen da suka mutu sakamakon nutsewar wani kwale-kwale dauke da bakin haure a Senegal ya kai 42, yayin da mutum guda ne kawai aka samu da rai.
Hukumar kashe gobara ta kasar ce ta tabbatar da hakan a ranar Laraba, 11 ga watan Nuwamba, 2026, inda ta ce ana ci gaba da aikin bincike da ceto a yankin gabar teku.
Lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Nuwamba a gabar tekun Thiéppe, kusa da kauyen Tébène 2, da ke karamar hukumar Kébémer a yankin Louga, arewa maso yammacin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa an gano gawarwaki hudu a ranar Juma’a, 17 a ranar Asabar, 14 a Lahadi, hudu a Litinin, biyu a Talata, sannan aka gano guda daya a Laraba, wanda ya kai adadin zuwa 42.
Hukumomin kasar sun kuma kafa wata tawagar ba da agajin gaggawa ta fuskar lafiya da tunani domin tallafa wa jami’an da ke aikin ceto da kuma iyalan wadanda suka rasu.