Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGhana ta cafke mutane sama da 100 kan zargin zambar intanet

Ghana ta cafke mutane sama da 100 kan zargin zambar intanet

An kama ƙungiyoyin da ke aikata zambar intanet a Ghana

Hukumomi a Ghana sun ce sun kama sama da mutum 100 waɗanda ake zargi da aikata zamba ta intanet a safiyar yau Asabar, a wani samame da aka kai yankunan Tabora da Lashibi, da ke Accra.

An kai samamen da nufin kama ƙungiyoyin da ke aikata zambar intanet da sauransu, inda lamarin ya kai ga kama mutane 141, yawanci ƴan Najeriya ne.

An kuma kama wani mutum ɗan asalin Ghana wanda ake zargi da bai wa mutanen da aka kama wurin zama.

Hukumomin ƙasar Ghana sun ce sun ƙwato kwamfutoci 38 da wayoyin salula 150 waɗanda ake amfani da su wajen aikatar zambar ta intanet.

A wani sako da ya wallafa a shafin X, Ministan sadarwa, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma fasaha na ƙasar, Sam George, ya ce ana zargin mutanen da aikata laifukan zamba daban-daban.

“Muna ci gaba da binciken wayoyin da muka ƙwace, kuma duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi bisa tsarin dokokin Ghana,” in ji Sam.

Samamen ya biyo bayan kama wasu mutum 48 ranar Laraba, abin da ke ƙara nuna ƙoƙarin da ƙasar ke yi wajen daƙile ayyukan masu zambar intanet.

Wani rahoto kan laifukan zamba na 2025 da hukumar yan sandan ƙasa da ƙasa na Interpol suka fitar, ya nuna cewa ayyukan masu zambar na ƙara girma a nahiyar Afirka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments