Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta haramta wa ’yan mata gudanar da sana’ar talla da daddare a faɗin jihar, inda ta umurce su da dakatar da ayyukansu kafin ƙarfe 10:00 na dare a kowace rana.
Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar, Sheikh Saifullahi Yakubu Musa, ne ya bayyana matakin a ranar Talata yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar.
Kwamandan ya bayyana cewa umarnin ya shafi ’yan matan da ke gudanar da sana’ar talla a jihar, inda ya ce dole ne su kammala ayyukansu kafin lokacin da hukumar ta kayyade.