Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada alƙawarinsa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya, tare da gode wa al’ummar Jihar Jigawa bisa goyon bayan da suke ba shi da jam’iyyar APC.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gangamin yaƙin neman zaɓen APC da aka gudanar a filin wasa na Dutse Township da ke Jihar Jigawa.
Ya ce gwamnatinsa na ƙara inganta walwala da albashin jami’an tsaro domin ƙarfafa musu gwiwa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa na ƙarfafa rundunonin soji da ’yan sanda, tare da tabbatar da cewa Najeriya za ta yi nasara kan waɗanda ke barazana ga zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasar.
A yayin gangamin, Tinubu ya gabatar da kundin manufofin APC mai taken “From Reforms to Prosperity”, wanda ya ƙunshi nasarorin gwamnatinsa da shirye-shiryenta a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, noma da tsaro.
Ya kuma kare matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa kuɗaɗen da aka samu daga matakin sun taimaka wajen gudanar da manyan ayyukan raya ƙasa.
Haka kuma, ya yi alƙawarin ƙara tallafa wa manoman ƙananan gonaki ta hanyar samar musu da lamuni marasa ruwa, injinan noma da inganta hanyoyin ban ruwa domin ƙara samar da abinci.
Kafin gangamin, Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da cibiyoyin koyon sana’o’i guda biyu, wato Bola Ahmed Tinubu Multi-Purpose Skills Acquisition Centre da Renewed Hope Technical Services Centre. Ya kuma ƙaddamar da hanyar Old Police Station zuwa Fadar Sarkin Dutse, mai tsawon kilomita uku, wadda aka mayar titin tagwaye.
Bugu da ƙari, shugaban ya ƙaddamar da taraktoci 400 da sauran kayan aikin gona da gwamnatin Jihar Jigawa ta saya domin bunƙasa noman zamani.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya gode wa Tinubu bisa ayyukan raya ƙasa da tallafin da jihar ke samu, ciki har da Greater Hadejia Water Project, kafa kwalejojin ilimi na tarayya a Dutse da Hadejia, shirin NELFUND da tallafin Conditional Cash Transfer ga iyalai masu ƙaramin ƙarfi.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da sauran jagororin APC sun buƙaci al’ummar Jigawa su ci gaba da goyon bayan gwamnatin Tinubu tare da zaɓen ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
Daga cikin manyan waɗanda suka halarci gangamin akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, tare da gwamnoni, ministoci da sauran shugabannin siyasa daga sassan ƙasar.