Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ce har yanzu ba ta samu sahihan kwafin hukuncin kotun tarayya kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC da kuma gabatar da takardun karatun Shugaba Bola Tinubu ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja, inda ya ce INEC ba ta dogara da rahotannin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta wajen ɗaukar mataki, sai dai sahihan takardun shari’a.
Dangane da hukuncin da ake cewa ya soke takarar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark, Amupitan ya ce hukumar ba ta samu kwafin hukuncin kotun da aka tabbatar da sahihancinsa ba.
Kan umarnin kotu da ya shafi gabatar da takardun karatun Tinubu, shugaban INEC ya ce zai ɗauki matakin da ya dace ne bayan an miƙa masa umarnin a hukumance, domin ya fara nazarin abin da kotun ta tanada.
Haka kuma, ya yi magana kan buƙatar samar da damar zaɓen tun da wuri ga ‘yan jarida, jami’an tsaro da ma’aikatan INEC da ke gudanar da ayyuka a ranar zaɓe, yana mai cewa har yanzu dokar zaɓe ba ta tanadi hakan ba, duk da cewa hukumar ta taɓa gabatar da shawarar ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
Amupitan ya kuma tabbatar da cewa jami’an rajistar masu zaɓe 54 da aka zarga da yin zagon ƙasa ga tsarin rajistar, ma’aikatan hukumar ne na cikakken lokaci, yana mai cewa INEC ba za ta ɓoye duk wani laifi da aka aikata ba.