Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiSarkin Musulmi ya sanar da fara watan Jumada Sani ranar Laraba

Sarkin Musulmi ya sanar da fara watan Jumada Sani ranar Laraba

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya sanar da cewa Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, ita ce ranar farko ta watan Jumada Sani na shekarar 1448 bayan hijira.

Sanarwar da Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, ya fitar ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, ta bayyana cewa ba a samu rahoton ganin jinjirin watan Jumada Sani daga kwamitocin duban wata a sassan Najeriya ba.

A cewar sanarwar, ranar Litinin ta yi daidai da 29 ga watan Jumadal Ula, amma kwamitin ba da shawara kan harkokin addini na majalisar tare da kwamitin duban wata na ƙasa ba su samu rahoton ganin sabon wata ba.

Saboda haka, Talata, 10 ga Nuwamba, za ta zama ranar cika kwanaki 30 na watan Jumadal Ula, kafin fara watan Jumada Sani a ranar Laraba.

Sanarwar ta ƙara da cewa Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya amince da rahoton kwamitin tare da ayyana Laraba a matsayin ranar farko ta sabon watan.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments