Tuesday, November 10, 2026
HomeKasuwanciWani kamfani ya zargi gwamnatin Kano da ƙoƙarin ƙwace masa fili na...

Wani kamfani ya zargi gwamnatin Kano da ƙoƙarin ƙwace masa fili na Naira biliyan 2

Wani kamfanin masana’antu mai suna A.B. Janruwa Enterprises da ke Kano, ya zargi gwamnatin jihar da fara ƙoƙarin ƙwace masa fili mai girman hekta sama da huɗu a yankin masana’antu na Chalawa ba tare da sanar da shi tun da farko ba.

Wani kamfanin masana’antu mai suna A.B. Janruwa Enterprises da ke Kano, ya zargi gwamnatin jihar da fara ƙoƙarin ƙwace masa fili mai girman hekta sama da huɗu a yankin masana’antu na Chalawa ba tare da sanar da shi tun da farko ba.

Kamfanin ya ce matakin na iya kawo cikas ga shirin faɗaɗa masana’antarsa, wanda aka tsara kashe biliyoyin nairori a kansa, kuma ana sa ran zai samar da ayyukan yi sama da 2,000.

Kamfanin, wanda ke ƙera zare da kayayyakin ɗinki, ya ce ya gano cewa ‘yan kwangilar gwamnati sun fara katange filin da aka ware domin faɗaɗa masana’antar, duk da cewa ba a sanar da shi a hukumance ko fara tsarin biyan diyya ba.

Manajan kamfanin, Abdullahi Hashim, ya shaida wa manema labarai cewa kamfanin ya sayi filin da ke kusa da masana’antarsa a Kirimbu, Chalawa, daga hannun manoma a tsawon shekaru domin gina babbar masana’anta.

Ya ce daga baya suka gano cewa an haɗa filin cikin sabon tsarin samar da yankin masana’antu da gwamnatin jihar ke shirin ginawa, wanda ke da alaƙa da hanyar bututun iskar gas ta Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK).

Lauyan kamfanin, Umar Ahmad Umar, ya ce gwamnati ba ta miƙa musu sanarwar soke mallakar filin kamar yadda doka ta tanada ba, kuma sai bayan an fara aiki a wurin suka samu labarin abin da ke faruwa.

Sai dai Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsaren Gine-gine ta Kano ta ce za a biya dukkan waɗanda abin ya shafa diyya yadda ya kamata.

Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar, Murtala Shehu, ya buƙaci kamfanin ya kwantar da hankalinsa, yana mai cewa ba za a ƙwace wani fili ba tare da biyan diyya ba, kuma aikin na da nufin bunƙasa tattalin arzikin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments