Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZa a kawo ƙarshen matsalolin tsaro a 2026 – Akpabio

Za a kawo ƙarshen matsalolin tsaro a 2026 – Akpabio

Akpabio ya bayyana cewa nan da shekarar 2026 za’a kawo karshen Yan bindiga da sauran matsalolin tsaro

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana kan matsalolin rashin tsaro a Najeriya.

Akpabio ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa za a kawar da ’yan bindiga da sauran matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan, nan da shekarar 2026.

Jaridar The Nation ta ce ya yi wannan kiran ne a wajen wani taron addu’a da azumi da aka shirya domin girmama iyalan Akpabio.

A cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai, Anietie Ekong, ya fitar, an ambato shugaban majalisar dattawan yana cewa: “Ina yi wa dukkan ’yan Najeriya fatan sabuwar shekara mai albarka da zaman lafiya.

Ina so na tabbatar wa ’yan Najeriya cewa sabuwar shekarar za ta zo da sabon salo na zaman lafiya a kasarmu.”

“Alfarmar haihuwar Yesu Almasihu, za a fanshi ’yan Najeriya daga ta’addanci, ’yan bindiga da masu tayar da kayar baya a sabuwar shekara da ma bayan ta.”

Shugaban Majalisar Dattawan ya bukaci ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyyun siyasa ba, da su mara wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a yaki da ’yan bindiga da ’yan ta’adda.

Akpabio ya nuna kwarin gwiwar cewa sabuwar hadin gwiwa da kasashen waje za ta taimaka wajen murkushe matsalolin tsaro.

Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da iyali ke takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba, inda ya ce hadin kai shi ne ginshikin nasarar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments