Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Sokoto ya yi bayanai game da harin Amurka ta kai Jihar

Gwamnan Sokoto ya yi bayanai game da harin Amurka ta kai Jihar

Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da kai wani hari a wasu sassan jihar, harin da Amurka ta ce an kai shi ne kan mayaƙan ƙungiyar IS.

Gwamnatin ta ce harin ya gudana ne a yammacin Alhamis, 25 ga Disamban 2025, inda ta bayyana cewa an yi aikin ne ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin sojojin Amurka da na Najeriya domin dakile barazanar tsaro a yankin.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar, ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala tantance cikakken sakamakon harin ba.

A cewarsa: “Ba za iya tantance haƙiƙanin sakamakon harin ba a cikin ƙanƙanin lokaci, saboda har yanzu muna jiran cikakken rahoton aiki na musamman.”

Sanarwar ta nuna cewa ana ci gaba da tattara bayanai daga hukumomin tsaro domin fahimtar abin da harin ya haifar, musamman dangane da wuraren da aka kai hari da kuma tasirin da ya yi.

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa harin da aka kai a yankin Jabo bai yi sanadin mutuwa ko jikkata fararen hula ba, lamarin da ta ce yana da matuƙar muhimmanci wajen kare rayukan al’umma.

Wannan bayani ya zo ne bayan rade-radin da suka fara yawo a wasu sassan jihar game da yiwuwar samun asarar rayuka, abin da gwamnati ta musanta.

Gwamnatin Sokoto ta bayyana goyon bayanta ga duk wani aikin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da wasu ƙasashe ko masu ruwa da tsaki, muddin manufarsa ita ce magance matsalolin tsaro da sauran laifuffuka a jihar.

A cewar sanarwar, irin wannan haɗin gwiwa na taimakawa wajen ƙarfafa jami’an tsaro da inganta dabarun da ake amfani da su wajen kare al’umma daga hare-hare.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments