Firimiyan jihar New South Wales, ya yi alkawarin kara samar da sauye sauye bayan da gwamnatinsa ta amince da wasu sabbin dokoki kan mallakar bindiga.
Chiris Minns, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne bayan harin da aka kai wa Yahudawa a wani wurin biki a gabar tekun Bondi, inda har mutum 15 suka rasa ransu.
Karkashin sabuwar dokar, mutum zai iya mallakar bindiga har guda hudu, manoma kuma za su iya mallakar sama da bindiga goma.
Sannan a kara wa yan sanda karfin ikon hana zanga-zanga.
Gwamnatin jihar ta ce wannan sabbin dokoki na mallakar bindiga su ne mafi tsauri da aka taba yi an Australia inda aka takaitawa mutane bindigogin za su iya mallaka.
Tuni dai masu suka ce zasu kalubalanci matakin hana zanga-zanga.