Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya sanar a ranar Alhamis cewa zai yi ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa a matakin ƙasa da ƙasa, yana da shekaru 41.
Ronaldo ya buga wa tawagar Portugal wasanni 234, inda ya zura ƙwallaye 146, lamarin da ya sanya shi kafa tarihi a matsayin ɗan wasan da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin ƙasashen duniya.
A kwanakin baya ne ɗan wasan ya fice daga sansanin tawagar Portugal, lamarin da ya janyo dakatar da shi na tsawon kwanaki 30.
Duk da rade-radin da ake yi cewa yana shirin ci gaba da buga wa ƙasarsa wasa, Ronaldo, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar, ya wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na Instagram a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa ya kawo ƙarshen taka leda a tawagar ƙasar.
A cikin saƙon nasa, Ronaldo ya ce: “Ya ku al’ummar Portugal, ranar ta zo da zan miƙa rigar mai lamba bakwai ta tawagar ƙasarmu ga waɗanda za su zo nan gaba.”
An nuna hotunan wasu muhimman lokutan da ya yi a fagen ƙwallon ƙafa a cikin faifan bidiyon da ya wallafa.