Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiTinubu ya nemi amincewar majalisa domin karɓo sabon bashin Dala biliyan 7.7

Tinubu ya nemi amincewar majalisa domin karɓo sabon bashin Dala biliyan 7.7

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓo sabon bashin kuɗaɗen waje har dala biliyan 7.7, kwatankwacin naira tiriliyan 10.79.

Tinubu ya gabatar da buƙatar ne ta cikin wata wasiƙa da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

A cikin wasiƙar, shugaban ƙasar ya bayyana cewa ana buƙatar kuɗaɗen ne domin taimakawa wajen cike gibin kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda ya kai naira tiriliyan 20.2.

Ya ce za a yi amfani da bashin wajen gudanar da ayyuka da shirye-shirye a muhimman fannoni da suka haɗa da tsaro, sufuri, noma, wutar lantarki, ilimi da lafiya.

Haka kuma, Tinubu ya bayyana cewa bashin zai taimaka wajen ƙara yawan ajiyar kuɗaɗen waje na Najeriya da kuma ƙarfafa darajar Naira.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments