Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiShugaban EFCC ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal kan ci gaban Zamfara

Shugaban EFCC ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal kan ci gaban Zamfara

Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya bayyana Jihar Zamfara a matsayin misali na shugabanci mai kawo sauyi a ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal.

Shugaban EFCC, Olanipekun Olukoyede, ya bayyana Jihar Zamfara a matsayin misali na shugabanci mai kawo sauyi a ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 30 da kafuwar jihar a Gusau, inda ya ce ya gudanar da bincike kan jihar kafin amincewa da gayyatar.

Olukoyede ya yaba da sabon filin jirgin sama, hanyoyin da aka shimfiɗa wa kwalta da fitilun kan tituna masu amfani da hasken rana. Ya kuma jinjinawa jihar kan ingantuwar sakamakon ɗalibai a jarrabawar NECO da WAEC.

A nasa ɓangaren, Gwamna Lawal ya ce ajandar gwamnatinsa mai ginshiƙai shida da shirin ci gaban Zamfara na 2025 zuwa 2034 za su taimaka wajen magance ƙalubalen jihar.

Ya buƙaci masu ruwa da tsaki su tabbatar da cewa shawarwarin da aka tattauna sun haifar da ci gaba a rayuwar al’umma, musamman ta fuskar tsaro, riƙon amana da tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments