Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiKashi 86 cikin 100 na kisan ’yan jarida a duniya ba a...

Kashi 86 cikin 100 na kisan ’yan jarida a duniya ba a warware su ba

Hukumar kula da ilimi, kimiyya da al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta bayyana cewa kashi 86 cikin 100 na kisan ’yan jarida a faɗin duniya ba a kammala bincikensu ko hukunta waɗanda suka aikata su ba.

UNESCO ta ce duk da sauye-sauyen barazanar da ’yan jarida ke fuskanta, rashin hukunta masu hannu a kisan nasu na ci gaba da zama babbar matsala.

Hukumar ta yi wannan kira ne yayin bikin ranar yaƙi da rashin hukunta masu aikata laifuka kan ’yan jarida ta duniya, inda ta buƙaci a ɗauki matakan kare rayukan ’yan jarida, kawo ƙarshen rashin hukunta masu laifi da kuma kare ’yancin aikin jarida.

Ta jaddada cewa duk ɗan jarida da aka kashe ko aka yi wa shiru, babbar asara ce ga al’umma baki ɗaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments