Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiAn kama wani mutum kan zargin koƙarin shigar da tabar wiwi gidan...

An kama wani mutum kan zargin koƙarin shigar da tabar wiwi gidan yarin Kurmawa a Kano

Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Najeriya ta kama wani mutum mai suna Nura Mohammed, mai shekaru 40, bisa zargin yunƙurin shigar da tabar wiwi cikin gidan yarin Kurmawa da ke Kano.

Sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar a Jihar Kano, Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, ya fitar, ta bayyana cewa wanda ake zargin mazaunin unguwar Janguza ne.

A cewar sanarwar, Nura ya yi yunƙurin jefa abin da ake zargin tabar wiwi ce cikin gidan yarin da misalin ƙarfe 12:00 na rana.

Sai dai jami’an gidan yarin da ke bakin aiki sun gano abin da ke faruwa, inda suka yi nasarar cafke shi kafin ya kai ga shigar da abin cikin gidan yarin.

Hukumar ta ce bayan kama shi, an miƙa Nura Mohammed ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) domin gudanar da bincike da kuma ɗaukar matakin da ya dace.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments