Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla ɗalibai mata 12 a makarantar Islamiyya ta Madarasatul Nurul Islam da ke ƙauyen Maikujeri, a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Asabar, 31 ga Oktoba, 2026, lokacin da ɗaliban ke aikin girbin masara a gonar malaminsu da ke wajen ƙauyen.
Wani mazaunin yankin, Mohammed Adamu, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa ’yan bindigar sun tare ɗaliban ne a lokacin da suke kan hanyar komawa gida, inda suka yi awon gaba da su.
Wata majiya da ke da kusanci da makarantar ta bayyana cewa baya ga ɗalibai mata 12, maharan sun kuma sace ƙanin mai makarantar, Malam Mainasara, lamarin da ya kai adadin waɗanda aka sace zuwa mutum 13.
Majiyar ta ce shekarun ɗaliban da aka sace sun kasance tsakanin tara zuwa 14, kuma an yi garkuwa da su ne a lokacin da suka tsaya a bakin wata rijiya domin shan ruwa da wanke jikinsu bayan sun gama aikin gona.
Haka kuma, an ruwaito cewa wani mai babur mai suna Tasi’u ya samu rauni bayan ’yan bindigar sun harbe shi lokacin da ya yi ƙoƙarin tserewa.
A halin yanzu yana karɓar magani a Asibitin Kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida da ke Minna.
Rahotanni sun kuma nuna cewa hare-haren ’yan bindiga sun ƙara shafar manoma a wasu yankunan jihar, inda wasu ke fuskantar matsalar shiga gonakinsu domin girbi saboda barazanar hare-hare da garkuwa da mutane.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai tantance bayanan kafin ya bayar da cikakken bayani.
Sai dai ya tabbatar da ceto wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Mahangi, ƙaramar hukumar Rafi, bayan wani samame da jami’an tsaro suka gudanar kusa da Pandogari a ranar 29 ga Oktoba.