Friday, November 6, 2026
HomeFasahaNajeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 4.6 sakamakon rushewar gine-gine – Rahoto

Najeriya ta yi asarar Naira tiriliyan 4.6 sakamakon rushewar gine-gine – Rahoto

Wani rahoto ya bayyana cewa Najeriya ta yi asarar aƙalla Naira tiriliyan 4.6 sakamakon rushewar gine-gine da lalacewar kayayyaki da kadarori tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025.

Wani rahoto ya bayyana cewa Najeriya ta yi asarar aƙalla Naira tiriliyan 4.6 sakamakon rushewar gine-gine da lalacewar kayayyaki da kadarori tsakanin shekarar 2022 zuwa 2025.

Shugaban hukumar CIFCFIN, Dr. Iliyasu Gashinbaki, ya ce wani binciken injiniyanci ya gano gine-gine 111 da suka rushe tsakanin 2015 zuwa 2025, inda mutane 321 suka mutu, yayin da wasu 344 suka jikkata.

Rahoton ya nuna cewa matsalolin sun haɗa da amfani da kayan gini marasa inganci, rashin ƙwarewar masu aikin gini, ƙarancin sa ido da kuma ƙoƙarin rage kuɗin da ake kashewa wajen gina gine-gine.

Gashinbaki ya ce asarar ta nuna buƙatar gudanar da bincike mai zurfi da kuma hukunta waɗanda aka samu da laifin sakaci ko yin amfani da dabarun da ke jefa rayukan jama’a cikin haɗari.

Ya kuma bayyana cewa an ƙaddamar da wani shiri tare da haɗin gwiwar hukumomin injiniyanci da bincike domin inganta sa ido, gano musabbabin rushewar gine-gine da kuma ƙarfafa ɗaukar matakan hukunta masu laifi.

A wani lamari makamancin haka, wani gini mai hawa biyar da ake ginawa a unguwar Wuse II da ke Abuja ya wani ɓangaren sa ya ruguje a ranar 17 ga Oktoba, 2026, inda ma’aikaci guda ya jikkata. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce ba a samu asarar rai ba.

Rahoton ya ba da shawarar cewa hukumomi su riƙa binciken ingancin kayan gini, sa ido kan ayyukan gine-gine a matakai daban-daban da kuma hukunta masana’antun da masu sana’ar gini da aka samu da karya ƙa’idoji, domin rage yawan rushewar gine-gine a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments