Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun kuɓutar da mutum 11 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a wasu ayyukan tsaro guda biyu da suka gudanar a yankunan Ribah da Wasagu-Falfala, cikin ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.
A ranar 30 ga Oktoba, 2026, sojojin sun bi sawun wasu ’yan bindiga da suka tare hanyar Ribah zuwa Dirindaji, inda suka tilasta musu sakin mutum bakwai da suka yi garkuwa da su, bayan maharan sun tsere zuwa yankin ƙauyen Rambo.
Sanarwar rundunar ta bayyana cewa an miƙa mutanen bakwai da aka ceto ga iyalansu.
A wani aikin tsaro na daban da aka gudanar a ranar 31 ga Oktoba, sojojin sun sake kuɓutar da wasu mutum huɗu bayan daƙile wani kwanton ɓauna da ’yan bindiga suka yi musu a hanyar Wasagu-Falfala.
A cikin sanarwar da mukaddashin jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Tamuno Sinivie, ya fitar, ya ce maharan sun tsere bayan martanin da sojojin suka mayar, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce an miƙa mutanen huɗu ga dagacin Wasagu, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri da ayyukan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.