Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaNajeriya na fuskantar matsanancin karancin jini – NBSA

Najeriya na fuskantar matsanancin karancin jini – NBSA

Hukumar Kula da Ayyukan Samar da Jini ta Ƙasa (NBSA) ta bayyana cewa Najeriya na fuskantar matsanancin ƙarancin jini, inda cibiyoyinta suka tattara rukunin jini tsakanin 24,000 zuwa 25,000 kacal a shekarar 2025.

Daraktan hukumar, Farfesa Saleh Yuguda, ya ce Najeriya na buƙatar rukunin jini tsakanin miliyan 1.8 zuwa miliyan biyu a duk shekara domin biyan buƙatun asibitoci a faɗin ƙasar.

Yuguda ya bayyana cewa ana buƙatar aƙalla kashi biyu cikin ɗari na al’ummar Najeriya su riƙa bayar da gudummawar jini bisa son rai domin rage gibin da ake fuskanta.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kan ’yan jarida kan muhimmancin bayar da jini bisa radin kai, inda Daraktan Ayyuka na hukumar, Dakta Aliyu Dahiru Waziri, ya wakilce shi.

A cewarsa, ƙarancin masu bayar da jini bisa son rai na jefa rayukan mata masu juna biyu da masu haihuwa, waɗanda suka samu haɗarin mota, masu fama da cutar sikila da sauran marasa lafiya cikin haɗari.

Hukumar ta kuma bayyana shirin ƙaddamar da tsarin tattara bayanan jini na zamani, wanda zai taimaka wajen bibiyar kowanne rukunin jini tun daga lokacin da aka bayar da shi har zuwa lokacin da aka yi wa mara lafiya ƙarin jinin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments