Tuesday, November 10, 2026
HomeLabaraiMataimakin shugaban ƙasa ya isa Ebonyi domin halartar gangamin kamfen ɗin APC

Mataimakin shugaban ƙasa ya isa Ebonyi domin halartar gangamin kamfen ɗin APC

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi, domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da ake gudanarwa a yau.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi, domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC da ake gudanarwa a yau.

Za a gudanar da gangamin ne a filin wasa na Pa Ngele Oruta Township Stadium, yayin da jam’iyyar ke ci gaba da neman goyon bayan al’umma gabanin zaɓen 2027.

A wata sanarwa da aka fitar, an bayyana cewa ziyarar na daga cikin ƙoƙarin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu da Kashim Shettima na ƙarfafa goyon bayan al’umma a jihar.

Sanarwar ta kuma ce gwamnatin Tinubu ta amince da ware naira biliyan 248 domin ƙarin ayyukan tituna a Ebonyi, ciki har da aikin faɗaɗa hanyar Enugu zuwa Abakaliki da Ogoja, da kuma gyaran wasu muhimman hanyoyi.

Haka kuma, ana ci gaba da aikin babbar hanyar Calabar–Ebonyi–Benue–Abuja, wadda aka tsara domin sauƙaƙa zirga-zirga da buɗe sabbin kasuwanni ga manoma da ’yan kasuwa.

An ce waɗannan ayyuka, tare da ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Gwamna Francis Nwifuru ke gudanarwa, na daga cikin abubuwan da APC ke gabatarwa yayin neman sake samun goyon bayan al’ummar jihar a zaɓen 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments