Ma’aikatan manyan makarantun gaba da sakandare mallakar gwamnatin jihar Taraba sun ayyana yajin aikin gargaɗi na makonni biyu domin matsa wa gwamnati ta biya musu buƙatunsu.
Shugaban ƙungiyar JACTI, Misa N. Gaji, da sakatarenta, Abdulkarim Z. Dangana, ne suka sanar da matakin bayan wani taro da suka gudanar a Jalingo ranar Alhamis.
Ƙungiyar ta ce ta ɗauki matakin ne bayan shafe sama da watanni huɗu tana tattaunawa da gwamnati ba tare da samun biyan buƙatunta ba, duk da wa’adin kwanaki 14 da ta ba ta tun da farko.
Buƙatun sun haɗa da dakatar da cire kuɗaɗe daga albashin ma’aikata ba tare da bayani ko samar da katunan shaida da fom ɗin APER ba, da kuma aiwatar da ƙarin albashi na shekara-shekara da ɗaga matakin aiki da aka kwashe sama da shekaru 10 ba a yi ba.
JACTI ta kuma yi barazanar cewa idan gwamnati ba ta magance matsalolin ba bayan wa’adin makonni biyu, za ta iya tsunduma yajin aikin sai baba ta gani bisa dokokin ƙwadago.