Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabarai’Yan sanda sun gargaɗi ’yan siyasa kan lalata hotunan abokan hamayya

’Yan sanda sun gargaɗi ’yan siyasa kan lalata hotunan abokan hamayya

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan lalata ko cire hotuna da allunan tallan abokan hamayyarsu, tare da umartar jami’anta da su gudanar da bincike tare da kama waɗanda ake zargi da aikata hakan a faɗin ƙasar.

Kakakin rundunar, Ani Iniedu, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Babban Sufeton ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, ya umarci kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da na Babban Birnin Tarayya Abuja da su ɗauki matakan dakile irin waɗannan ayyuka.

Sanarwar ta ce umarnin ya zo ne a daidai lokacin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda rundunar ta buƙaci jami’an tsaro su binciki duk wani rahoto da ya shafi lalata kayan tallan siyasa.

Rundunar ta kuma bayyana cewa lalata ko cire hotunan ɗan takara ba bisa ƙa’ida ba na iya zama laifi ƙarƙashin sashe na 451 na Criminal Code Act da kuma sashe na 326 na Penal Code Law.

Haka kuma, ta ce za a gudanar da bincike kan duk wanda aka samu hujjar cewa ya ɗauki nauyin irin waɗannan ayyuka, tare da gurfanar da waɗanda aka tabbatar sun aikata laifi a gaban kotu.

A ƙarshe, rundunar ta buƙaci jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su mutunta haƙƙin juna, tare da gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe cikin lumana da bin doka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments