Friday, November 6, 2026
HomeIlimiJami’ar PAMO da ke jihar Rivers ta shiga ƙungiyar jami’o’in duniya

Jami’ar PAMO da ke jihar Rivers ta shiga ƙungiyar jami’o’in duniya

Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta PAMO da ke Fatakwal, jihar Rivers, ta shiga ƙungiyar jami’o’in duniya ta Oxonia University Network, wadda ke inganta haɗin gwiwar ilimi, bincike da ƙirƙire-ƙirƙire.

Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta PAMO da ke Fatakwal, jihar Rivers, ta shiga ƙungiyar jami’o’in duniya ta Oxonia University Network, wadda ke inganta haɗin gwiwar ilimi, bincike da ƙirƙire-ƙirƙire.

Jami’ar ta bayyana hakan ne bayan wani taron shugabanci da amfani da fasahar zamani ta AI a manyan makarantu da aka gudanar a Jami’ar Oxford da ke Birtaniya.

Ƙungiyar, wadda aka kafa a shekarar 2013 da jami’o’i 16 daga ƙasashe 14, yanzu ta ƙunshi jami’o’i sama da 153 daga ƙasashe 41.

Shigar PAMO zai ƙara wa ƙungiyar ƙarfi a Afirka da Asiya, tare da ba ta damar bayar da gudummawa a fannin koyar da ilimin likitanci da binciken kiwon lafiya.

A yayin taron, shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), Farfesa Abdullahi Yusufu Ribadu, ya karɓi shugabancin ƙungiyar daga Farfesa Abubakar Rasheed, inda ya bayyana shirin bunƙasa amfani da fasahar AI a koyarwa, gudanarwa da binciken likitanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments