Dakarun Sojojin Najeriya, tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), sun kama wani mutum mai suna Mukaila Iliyasu bisa zargin barazanar sace wata mata domin karɓar kuɗin fansa a jihar Nasarawa.
An kama wanda ake zargin ne a garin Akwaba da ke ƙaramar hukumar Eggon, yayin da yake ƙoƙarin karɓar kuɗi har Naira 200,000 da ake zargin ya nema daga matar domin kada ya sace ta.
Rahoton jaridar Daily Trust ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan samun bayanan sirri kan barazanar da Iliyasu ya yi.
Mukaddashin jami’in yaɗa labarai na Operation Whirl Stroke, Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, ne ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta ce jami’an DSS sun sanar da sojoji game da barazanar a ranar 29 ga Oktoba, inda aka shirya samame na musamman domin kama wanda ake zargin da kuma hana yiwuwar sace matar.
Domin kama shi, wani soja ya shiga aikin basaja, inda ya yi kamar shi ne mutumin da aka tura domin kai kuɗin. Hakan ya taimaka wajen cafke Iliyasu a daidai lokacin da yake karɓar kuɗin, inda aka ƙwato Naira 200,000 da ake zargin kuɗin fansa ne.
Bayan kama shi, an miƙa wanda ake zargin ga jami’an DSS domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.
Kwamandan Operation Whirl Stroke, Manjo Janar Moses Kolo Gara, ya yaba wa sojoji da jami’an DSS bisa haɗin gwiwar da suka nuna, tare da kira gare su da su ci gaba da musayar bayanan sirri domin dakile garkuwa da mutane da sauran laifuffuka.