Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.
Yari ya ce tarihin ayyukan gwamnatin Tinubu, tare da ƙoƙarin kwamitin yaƙin neman zaɓen APC na wayar da kan al’umma, za su taimaka wajen neman goyon bayan ’yan Najeriya domin sake zaɓen shugaban ƙasar.
Ya bayyana cewa yana dogaro da Allah wajen ganin Tinubu ya samu nasara kamar yadda ya faru a zaɓen 2023, yana mai cewa wajibi ne ’yan siyasa su haɗa addu’a da ƙoƙarin neman goyon bayan jama’a.
Yari ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Makka da ke ƙasar Saudiyya, inda ya raka Tinubu da wasu manyan ’yan Najeriya gudanar da ƙaramin aikin Hajji, wato Umrah.
Ya ƙara da cewa kwamitin yaƙin neman zaɓen APC zai ci gaba da wayar da kan al’umma tare da bayyana ayyukan gwamnatin Tinubu domin ƙarfafa goyon bayan sake zaɓen shugaban ƙasar a 2027.