Darakta-Janar na ƙungiyar Arewa For Asiwaju (A4A), Mohammed Badaru Abubakar, ya gana da tawagar malaman Musulunci da ƙwararru domin tattauna batutuwan haɗin kai, ci gaban matasa da kuma goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Siraj Abdulkarim, wanda shi ne shugaban ƙasa na ƙungiyar Community and Youth Development (CYD), ta ziyarci Badaru a ofishinsa da ke Garki, Abuja.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɗin kan al’ummar Musulmi, zaman lafiya, ci gaban matasa da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin addini.
Haka kuma, ɓangarorin sun duba hanyoyin haɗa kai domin tallafa wa sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.
A yayin ganawar, sun jaddada muhimmancin haɗin kai, shugabanci nagari da haɗin gwiwa wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a Najeriya, tare da bayyana aniyarsu ta ci gaba da tattaunawa da aiki tare domin cimma manufofin da suka sanya a gaba.