Hukumomin tsaro a Najeriya sun kuɓutar da limaman addinin Musulunci uku daga cikin shida da ’yan bindiga suka sace a Jihar Zamfara.
An sace limaman ne ranar 12 ga Satumba, 2026, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Talata Mafara domin halartar addu’a ta musamman ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun tare su da misalin ƙarfe 11:30 na safe a hanyar Dakko-Damri, kusa da dajin Sububu, a Ƙaramar Hukumar Bakura ta jihar.
Wani babban jami’in tsaro da ke da hannu a aikin ceto ya ce an kuɓutar da limaman cikin ƙoshin lafiya, sakamakon aikin da hukumomin tsaro suka gudanar bisa bayanan sirri. An kuma yi musu gwajin lafiya kafin a miƙa su ga gwamnatin jihar domin haɗuwa da iyalansu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Zamfara, Ahmad Muhammad Bello, ya tabbatar da kuɓutar da limaman, tare da yaba wa haɗin gwiwar Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), DSS da ’yan sanda.
A halin yanzu, hukumomin tsaro na ci gaba da ƙoƙarin kuɓutar da sauran limaman uku da ke hannun masu garkuwa da mutane, tare da kamo waɗanda suka aikata laifin. An kuma buƙaci jama’a su taimaka da sahihan bayanai domin yaƙi da ’yan bindiga a yankin.