Abba Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin yin aiki domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC a zaɓen 2027, musamman a Jihar Adamawa.
Abba ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a hedikwatar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja, yayin wani taron manema labarai na ƙaddamar da ƙungiyar Haske Bola Tinubu Organisation (HBTO), tare da bayyana manufofinta da hangen nesanta.
A yayin taron, ƙungiyar ta kuma ƙaddamar da shirin samar da sufuri a farashi mai rahusa ga al’umma a Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
Abba Atiku, wanda ya kafa ƙungiyar kuma yake jagorantarta, ya ce goyon bayan da yake bai wa Tinubu zaɓin siyasa ne da ya yi da kansa, bisa ƙudurinsa da abin da ya yi imani da shi.
Ya bayyana cewa ya fahimci yadda matakin nasa zai jawo hankalin jama’a, musamman kasancewar mahaifinsa ɗan takarar shugaban ƙasa ne a wata jam’iyyar siyasa.
Sai dai ya jaddada cewa ra’ayin siyasa ya shafi tunanin mutum, lamirinsa da ’yancin kowane mutum na yanke shawara ba tare da tilastawa ba.
Ya ce kafa da jagorantar HBTO mataki ne da ya ɗauka da gangan bisa cikakken imani da alkiblar siyasar da ƙungiyar ta zaɓa.