Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki a rikicin Iran da su rungumi hanyar diflomasiyya, yana mai cewa amfani da ƙarfin soji ba zai kawo ƙarshen yaƙin ba.
Merz ya bayyana hakan ne a yayin kammala ziyarar da ya kai Koriya ta Kudu a ranar Juma’a, inda ya buƙaci ɓangarorin da ke rikicin su fahimci cewa babu mafita ta soja ga rikicin.
A cewar kamfanin dillancin labaran Jamus (DPA), Merz ya ce ƙasarsa na ƙoƙarin haɗa kai da sauran ƙasashe domin ƙara ƙaimi ga ƙoƙarin diflomasiyya ta hanyoyi daban-daban, don ganin an kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa.
Ya kuma bayyana cewa Jamus na son ganin an kawo ƙarshen rikicin cikin sauri, musamman saboda tasirin da yake yi ga tattalin arziki.
Shugaban gwamnatin ya ce tashin farashin makamashi sakamakon rikicin ya riga ya jawo wa ƙasashen Turai asarar da ta haura Euro biliyan 100.