Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiRonaldo ya kusa kai ƙwallaye 1,000 bayan hat-trick da yayi a yau

Ronaldo ya kusa kai ƙwallaye 1,000 bayan hat-trick da yayi a yau

Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye uku a wasan da Al Nassr ta doke Al Kholood da ci 5-3 a gasar Saudi Pro League ranar Alhamis.

Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye uku a wasan da Al Nassr ta doke Al Kholood da ci 5-3 a gasar Saudi Pro League ranar Alhamis.

Ronaldo mai shekara 41 ya yi hakan ne kwana ɗaya bayan an ba shi kyautar Ballon d’Or of All Time (BOAT) ta mujallar France Football.

Kwallayen sun kai adadin da ya ci a rayuwarsa zuwa 985, inda yanzu ya rage masa ƙwallaye 15 kacal ya kai 1,000.

Kyaftin ɗin Al Nassr ya zura dukkan kwallayen nasa a rabin lokaci na biyu, bayan kungiyoyin biyu sun tashi kunnen doki da ƙwallaye biyu-biyu.

Ya fara da ƙwallon da João Félix ya ba shi, sannan ya ci ta biyu da kai bayan an haɗa masa ƙwallo. Daga bisani, Sadio Mané ya taimaka masa wajen zura ƙwallonsa ta uku.

Wannan ne karon farko da Ronaldo ya ci kwallaye uku a wasa ɗaya a wannan kakar. Ya zuwa yanzu, ya ci ƙwallaye takwas a gasar lig da tara a dukkan gasa a wannan kakar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments