Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta amince da tsohon minista Isa Ali Pantami da ɗan takarar gwamnan Kano na NDC, Abdulsalam Gwarzo, domin su tsaya takarar zaɓen 2027. Sai dai amincewar tana jiran sakamakon shari’o’in da ke gaban kotu.
A gefe guda, INEC ta ƙi amincewa da ƙorafin ɗan takarar gwamnan Ogun na PDP, Ladi Adebutu, wanda ya nemi a sake duba matakin cire sunansa daga jerin ’yan takara.
Wata majiya a hukumar ta shaida wa Daily Trust cewa INEC ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 69 daga jam’iyyun siyasa kan cire sunayen ’yan takara. Kimanin 36 daga cikinsu ne aka amince da su.
Hukumar ta ce cire sunayen ya danganci zargin rashin bin Dokar Zaɓe ta 2026, musamman batun miƙa rajistar ’yan jam’iyya, kamar yadda hukuncin Kotun Ƙoli ya tabbatar.
Gwarzo ya garzaya kotu domin ƙalubalantar cire sunansa da na mataimakinsa, Rabiu Mustapha. Shi ma Pantami na fuskantar shari’a kan takararsa, yayin da INEC ke shirin fitar da sanarwa a hukumance kan sakamakon bitar ƙorafe-ƙorafen.