Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiAn kama Malam Keya a Fatakwal kan zargin ɗaukar nauyin rikicin daba...

An kama Malam Keya a Fatakwal kan zargin ɗaukar nauyin rikicin daba a Dala da kewaye

Kwamitin yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da safarar haramtattun kayayyaki na jihar Kano ya kama wani mutum da aka fi sani da Malam Keya a birnin Fatakwal na jihar Rivers.

Kwamitin yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi da safarar haramtattun kayayyaki na jihar Kano ya kama wani mutum da aka fi sani da Malam Keya a birnin Fatakwal na jihar Rivers.

An kama shi ne bisa zargin shirya wa da ɗaukar nauyin ayyukan tashin hankali da suka shafi rikicin daba a Dala, wanda ya jawo rashin zaman lafiya a wasu sassan jihar Kano.

Shugaban kwamitin haɗin gwiwar hukumomin ya jagoranci aikin kama wanda ake zargin, wanda ya ƙunshi haɗin gwiwar jami’an da ke yaƙi da shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Kwamitin ya bayyana cewa kamen wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Kano na gano waɗanda ake zargin suna ɗaukar nauyin tashin hankali da kuma tarwatsa hanyoyin sadarwar masu aikata laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi.

Shugaban kwamitin ya ce za su ci gaba da bin diddigin duk wanda ake zargin yana barazana ga zaman lafiyar Kano, ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments