Jam’iyyar ADC ta ɗage ƙaddamar da kamfen ɗinta na shugaban ƙasa a jihar Sakkwato, wanda aka shirya gudanarwa ranar Asabar, 31 ga Oktoba, zuwa Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.
Daraktan Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a jihar, Hon. Bello Aliyu Goronyo, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Goronyo ya ce an ɗauki matakin ne domin warware wasu matsalolin tsare-tsare da daidaita shirye-shiryen gudanar da taron yadda ya kamata.
Ya nemi afuwar duk waɗanda sauyin ranar zai iya shafa, tare da gode wa shugabannin jam’iyyar, masu ruwa da tsaki da magoya bayanta bisa fahimta da goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen ya buƙaci duk waɗanda abin ya shafa su lura da sabuwar ranar, yana mai cewa yana fatan taron zai samu halartar shugabannin jam’iyyar, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki.