Friday, November 6, 2026
HomeSiyasaADC ta yi gargaɗi kan zargin shirin sauya ranar zaɓen shugaban ƙasa...

ADC ta yi gargaɗi kan zargin shirin sauya ranar zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC ya yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na sauya ranar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 16 ga Janairu, 2027.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC, Phrank Shaibu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Shaibu ya yi zargin cewa ana iya amfani da barazanar barkewar cutar Ebola a matsayin hujjar sauya jadawalin zaɓen, yana mai nuna damuwa kan yiwuwar faruwar hakan.

Ya kuma buƙaci shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, da kada ya amince da duk wani yunƙuri na sauya ranar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments