Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiAbdulsamad BUA ya karɓi ziyarar bazata daga tsohuwar matarsa, Hannatu Musawa

Abdulsamad BUA ya karɓi ziyarar bazata daga tsohuwar matarsa, Hannatu Musawa

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdulsamad BUA, ya bayyana cewa ya samu ziyarar bazata daga tsohuwar matarsa, Ministar Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-ƙirƙire ta Najeriya, Hannatu Musawa, a ofishinsa da ke Abuja.

A wani saƙo da ya wallafa, BUA ya ce duk da sauye-sauyen da lokaci ke kawowa, abota da mutunta juna suna nan daram a tsakaninsu.

Ya bayyana farin cikinsa kan ganawa da Musawa, yana mai yabawa da himma da sadaukarwar da take nunawa wajen bunƙasa al’adu da tattalin arzikin masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire na Najeriya.

Ya kuma yi mata fatan ci gaba da samun nasara a ayyukanta na hidimtawa ƙasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments