Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta ƙaddamar da farautar waɗanda suka kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Ibrahim Masussuka, da abokinsa Adamu Abubakar.
Rahotanni sun ce an harbe mutanen biyu ne a gaban gidan malamin da ke ƙaramar hukumar Dutsin-Ma a yammacin Litinin, lokacin da wasu ’yan bindiga biyu suka zo kan babur suka buɗe musu wuta, sannan suka tsere.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce an garzaya da waɗanda abin ya shafa zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar da rasuwarsu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ali Umar Fage, ya bayar da umarnin tura jami’an tsaro
zuwa yankin domin kamo waɗanda suka aikata kisan. Ya kuma tabbatar da cewa ana gudanar da bincike tare da ƙara ƙaimi wajen gano waɗanda ake zargi.