Friday, November 6, 2026
HomeLabaraiLabaraiMajalisar Kano ta amince da naɗin sabbin kwamishinoni shida

Majalisar Kano ta amince da naɗin sabbin kwamishinoni shida

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da naɗin sabbin kwamishinoni shida da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa mata domin tantancewa da tabbatar da naɗinsu.

Waɗanda majalisar ta amince da naɗinsu sun haɗa da tsohon Air Commodore Salisu Yusha’u, Hon. Ibrahim Namadi, Farfesa Sani Lawan, Hon. Muktar Ishaq Yakasai, Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa da Hon. Idris Garba Mustapha.

An gudanar da tantancewar ne a zaman majalisar na ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2026, ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore.

A yayin zaman, kakakin ya sanar da ’yan majalisar sunayen mutanen da gwamnan ya miƙa domin tantancewa.

Bayan kowannensu ya gabatar da kansa a gaban majalisar, ’yan majalisar sun bayyana gamsuwarsu da ƙwarewarsu, cancantarsu da gogewarsu wajen gudanar da ayyukan da aka naɗa su domin yi.

Sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar ta bayyana cewa ’yan majalisar sun yi la’akari da cancantar waɗanda aka zaɓa da kuma gudummawar da za su iya bayarwa wajen ci gaban jihar.

Daga cikin ’yan majalisar da suka ba da gudummawa yayin tattaunawar akwai wakilan Doguwa, Tudun Wada, Fagge, Kiru, Madobi, Dala da Aliyu Bagwai/Shanono.

A ƙarshen zaman tantancewar, majalisar ta amince da dukkan sunayen kwamishinonin shida, lamarin da ya share fage ga mataki na gaba na naɗa su a hukumance da kuma tura su ma’aikatun da za su jagoranta.

Ana sa ran sabbin kwamishinonin za su taka rawa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar Kano bayan an kammala sauran matakan naɗinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments