Rundunar ’yan sandan jihar Delta ta kuɓutar da wani mutum da wasu da ake zargi da garkuwa da mutane suka sace a jihar.
Mai magana da yawun rundunar, Bright Edafe, ya ce an sace mutumin ne ranar 19 ga Oktoba, 2026, a gaban gidansa da ke yankin Owa-Alero, inda aka tafi da shi cikin daji.
Ya ce ɗan’uwan wanda aka sace ne ya kai rahoton lamarin ga ’yan sanda, bayan wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane sun yi awon gaba da shi.
A cewarsa, jami’an rundunar daga ofishin ’yan sanda na Owa-Oyibu, tare da haɗin gwiwar masu sa-kai na yankin, sun gudanar da bincike a dazukan da ke kusa, har suka kuɓutar da mutumin ranar 20 ga Oktoba.
Edafe ya ce jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargi da aikata laifin, waɗanda suka tsere, domin gurfanar da su a gaban shari’a.